JAMA’AR ƊAN ALLAH, KU TARU

Magana: , cir­ca 1743 (Adeste, Fi­del­es).

Kidi: .


Jama’ar Ɗan Allah, Ku Taru ku yi murna,
Ku taru, ku taru a Baitalahmi.
Zo mu gaishe shi, Sarkin mala’iku.

Refrain

Mu yi masa sujada, mu yi masa sujada,
Mu yi masa sujada, Mai Centonmu.

Zo dai ku gan shi, jariri marar ƙarfi,
Yesu Ɗan Allah ne Madauwami.
Aka haife shi, ba a halicce shi ba.

Refrain

Rundunan Sama, yi ta rera waƙa,
Can cikin Sama ku ke yabonsa,
Yabo ga Allah, yabo kuwa ga Ɗansa.

Refrain

I, Ubangiji, kai ne mu ke yabo
Gaisuwa mai gaskiya mu ke yi maka.
Kai, Kalmar Allah, cike da alheri.

Refrain